NE

News Elementor

An Soki Kudurin Gwamnatin Tarayya Na Dawo Da Tsoffin Malaman Makaranta Bakin Aiki

Masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi sun kalubalanci yunkurin gwamnatin tarayya na sake mayar da malaman da suka yi ritaya a bakin aiki domin magance karancin malaman da ake fuskanta, inda suka yi gargadin cewa hakan ba zai haifar da kyakkyawan sakamako ba.

Kudurin, dake kunshe a sabon daftarin ilimi wanda ma’aikatar ilimi ta tarayya ta gabatar a shekarar 2025, na da manufar karfafa kwazon malamai, da daukar sabbin ma’aikata da kuma kula da su.

To sai dai, masu ruwa da tsaki na ci-gaba da bayyana damuwa kan wannan yunkurin.

Shugaban cibiyar ilimi ta Boar Tutors, Mr Temitope Peter, ya ce duk da yake yunkurin abu ne mai kyau, amma kuma babu tabbaci kan ko zai yi wani tasiri.

Kazalika, wata malama mai suna Mrs Adeyinka Adetunji, ta soki wannan yunkurin, wanda ta bayyana a matsayin matakin da bai dace ba.

Ta ce malaman da suka yi ritaya za su wahala sosai kafin su saba da harkokin ilimi na zamani, musamman a yanzu da komai ya koma kan na’ura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM