NE

News Elementor

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan ɗaki ɗaya su uku a kan hanyar kai gawar mahaifiyar su a Benue

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu yan uwa ciki ɗaya sj uku a karamar hukumar Ohimini da ke jihar Benue, yayin da suke kan hanyarsu daga Abuja zuwa garinsu domin kai gawar mahaifiyarsu da ta rasu domin a yi mata jana’iza.

Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar a kan titin Ogobia–Otukpo, bayan motar da suke ciki ta samu matsala, lamarin da ya tilasta musu tsayawa a hanya.

Bayan an gyara motar suka ci gaba da tafiya, sai suka ci karo da maharan, wadanda suka yi garkuwa da ‘yan uwan uku. An ce mazauna yankin sun ji karar harbe-harbe tsakanin karfe 3:00 zuwa 4:00 na asubahin ranar.

Shugaban karamar hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ya nufi wurin domin tantance abin da ya faru.

Daily Trust ta ce har zuwa lokacin hada rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Benue ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM