NE

News Elementor

Yar takarar gwamnan Gombe a PDP Monica Kaltho ta janye ƙarar da ta shigar kan Pantami tare da mara masa baya

Tsohuwar mai neman takarar gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar PDP, Monica Yahaya Kaltho ta janye ƙarar da ta shigar kan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, tare da bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar gwamna na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, gabanin zaɓen 2027.

A cewar jaridar The Punch, Kaltho ta ce ta ɗauki matakin ne bayan tuntuba da kuma girmama roƙon jagoran PDP a jihar, tsohon gwamna Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, domin tabbatar da haɗin kan jam’iyyar.

A nasa ɓangaren, Pantami ya yaba da matakin nata, yana mai cewa hakan alama ce ta kishin jam’iyya da nuna dattako, tare da alƙawarin haɗa kan dukkan masu ruwa da tsaki domin cimma nasara a zaɓen 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM