Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya amince da ƙarin albashi da alawus-alawus ga sarakunan gargajiya a faɗin jihar.
A cewar ƙungiyar ALGON, reshen Jihar Kaduna, wannan amincewa ta shafi manyan sarakuna, ciki har da sarakunan dauloli da manyan hakimai, da kuma dagatai da masu unguwanni.
Ƙungiyar ta yaba wa gwamnan kan wannan mataki, inda ta bayyana shi a matsayin abin da zai ƙarfafa hukumomin gargajiya da kuma rawar da suke takawa wajen inganta zaman lafiya, tsaro da ci gaban al’umma.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Sheikh Jamilu Abubakar Albani, ya fitar, ALGON ta ce sarakunan gargajiya na ci gaba da kasancewa abokan hulɗa da gwamnati da ba za a iya yin watsi da su ba wajen gudanar da mulki, tare da taka muhimmiyar rawa wajen haɗa gwamnati da al’umma.