‘Yan bindiga sun ƙaƙaba wa kauyukan Sokoto harajin Naira miliyan 40 tare da barazanar kai masu hari
Mazauna garin Kebbe da ke ƙaramar hukumar Kebbe a Jihar Sokoto na cikin fargaba, bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun nemi al’ummar garin su biya su Naira miliyan 40, tare da barazanar kai hari idan ba a biya kuɗin ba.
An ce ‘yan bindigar sun isar da wannan saƙo ne ta hannun wani mazaunin garin mai suna Abara Jaji, wanda suka tare a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa neman itace.
Wata majiya daga yankin ta shaida wa Daily Trust cewa Jaji yana tafiya ne a wata hanya da ake zargin ‘yan bindigar ke amfani da ita, lokacin da ya hango su ya kuma gudu, inda ya bar babur ɗinsa.
Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun bi shi a kan babura, suka cim masa sannan suka kewaye shi.
A cewar majiyar, ‘yan bindigar sun tambayi Jaji daga ina yake. Jaji, wanda aka ce tsoro ya kama shi, ya gaya musu cewa shi ɗan Kebbe ne, tare da roƙonsu cewa ba shi da kuɗi.
Daga nan ne ‘yan bindigar suka ba shi wata wayar Tecno mai ɗauke da SIM, suka umarce shi da ya kai wayar ga Sarkin Kebbe ko wakilinsa.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun nemi al’ummar garin ta biya Naira miliyan 40, tare da barazanar kai hari garin da kuma ƙona kadarori idan ba a biya kuɗin ba.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Jaji ya isa gidan Sarkin Kabin Kebbe, Alhaji Muhammad Labbo Margai, da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Talata, inda ya tarar da wakilinsa, Murtala Muhammad.
Ya ce Jaji ya bayyana masa cewa ‘yan bindigar ne suka aiko shi da wayar.
A cewar ganau, daga bisani ‘yan bindigar sun kira wayar tare da sake maimaita buƙatarsu ta Naira miliyan 40.
An ce Murtala ya gaya wa masu kiran cewa batun ya shafi al’ummar garin baki ɗaya, don haka ba zai iya yanke hukunci shi kaɗai ba.
Daga nan ne ya kai Jaji wajen DPO, inda wasu jami’an tsaro na ƙaramar hukumar su ma suke wurin.