NE

News Elementor

Atiku ya nuna damuwa kan yadda wasu matasa ke sayar da ƙodar su a Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa kan rahotannin da ya ce yana samu da ke cewa wasu matasan Najeriya na sayar da ƙodarsu kan kusan naira miliyan 1.7, inda ya ce wannan na daga cikin mummunan yanayin da ƙasar ke ciki.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Atiku ya ce halin da matasan Najeriya ke ciki ya kai matsayin da wasu ke tunanin ɗaukar matakan da ba za su taɓa tunanin ɗauka ba domin kawai su samu abin rayuwa.

Ya ce ya samu labarai masu tayar da hankali kan yadda wasu matasa ke shiga mawuyacin hali domin neman hanyar tsira.

Ya ce daga cikin mafi tayar da hankali akwai rahotannin da ke cewa wasu matasa na sayar da sassan jikinsu, musamman ƙoda, domin samun kuɗi.

Atiku ya ce idan tsadar rayuwa ta kai wani mataki da ba za a iya jurewa ba, matsanancin hali na iya sa abin da a da mutum ba zai taɓa tunanin aikatawa ba, ya yi tunanin aikatawa.

Ya dora alhakin tashin farashin abinci, sufuri, haya, kuɗin makaranta, magunguna da wutar lantarki kan tsarin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM