Dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar ADC, Alhaji Ibrahim Ali Amin Little, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa wasu ’yan jarida da ke ɗaukar rahoto kan gangamin jam’iyyar APC a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Little ya bayyana harin a matsayin abin takaici da rashin amincewa, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen daba da ta’addancin siyasa a jihar.
Ya ce abin damuwa ne yadda wasu ’yan siyasa ke zargin ɗaukar ’yan daba da amfani da su wajen gudanar da gangamin siyasa, yana mai cewa hakan na jefa matasa cikin aikata laifuka da sauran munanan halaye.
Dan takarar ya kuma ce bai kamata gangamin siyasa ya zama wajen tashin hankali da aikata laifuka ba, sai dai ya kasance wurin da jam’iyyu ke gabatar da manufofinsu, tattaunawa da jama’a da neman goyon bayansu.
Little ya jajanta wa Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ’yan jaridan da lamarin ya shafa, tare da nuna goyon baya ga sauran waɗanda harin ya rutsa da su.
Ya yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Kano, gwamnatinsa za ta kasance da manufar rashin sassauci ga daba da tashin hankalin siyasa, tare da ba da fifiko wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma yi alƙawarin samar da yanayin da ’yan jarida da sauran ’yan kasa za su gudanar da ayyukansu cikin ’yanci da tsaro, ba tare da tsoro ko barazana ba.