Wasu ’yan gwagwarmaya sun kafa gangamin Tinubu Must Go domin wayar da kan ’yan Najeriya kan burinsu na ganin an kawo ƙarshen mulkin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta hanyar zaɓen 2027.
Daya daga cikin jagororin gangamin, kuma lauya mai zaman kansa, Barr. Hamza Nuhu Dantani, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da Arewa Updates.
Dantani ya ce, sun kafa gangamin ne saboda ba su gamsu da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiya ba, yana mai iƙirarin cewa daga cikin alkawuran da shugaban ƙasar ya yi bai aiwatar da ko kaso biyar cikin 100 ba.
Ya kuma bayyana cire tallafin man fetur a matsayin ɗaya daga cikin dalilan kafa gangamin, yana mai cewar hakan ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Ya ce, Tinubu Must Go gangami ne na wayar da kan jama’a ba ƙungiya mai tsarin shugabanni da muƙamai ba, inda manufarsu ita ce mutum ya wayar da kan wani domin samun goyon bayan jama’a gabanin zaɓen 2027.
Dantani ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da yi wa ’yan adawa da masu sukarta bi-ta-da-kulli da kuma ɗaukar matakan da ya ce sun saɓa wa dimokuraɗiyya, yana mai bayar da misali da dakatar da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara na tsawon wata shida a lokacin dokar ta-ɓaci ta 2025 wanda fadar Shugaban Ƙasa ta ce an ɗauki matakin ne saboda rikicin siyasa da matsalar gudanar da gwamnati a jihar.
Da kafar yaɗa labarai ta Arewa Updates ta tambaye shi ɗan takarar da gangamin yake son marawa baya a 2027, Dantani ya ce ba su zaɓi wani ba a yanzu, amma suna fatan jam’iyyun adawa su haɗe domin samar da ɗan takara guda ɗaya da zai fafata da Tinubu.