‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 28 a lokacin da suka kai hari a kauyen Kagara da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sokoto, a daren Asabar.
Harin, wanda ya fara da misalin ƙarfe 8:58 na dare, ya ɗauki kusan tsawon sa’o’i uku, inda mazauna yankin suka ce ‘yan bindigar sun ci gaba da harbe-harbe har zuwa misalin ƙarfe 12:00 na dare.
Ɗaya daga cikin mutanen da aka kashe shi ne Abdullahi Lawwali, wanda ke fama da matsalar tabin hankali.
Wani mazaunin yankin ya ce a baya Lawwali ya samu kulawa a Asibitin Ƙwararrun Cututtukan Ƙwaƙwalwa na Tarayya da ke Kware, Jihar Sokoto.
Mazaunin ya ce an kashe Lawwali ne bayan ya ƙi bin ‘yan bindigar lokacin da suka yi ƙoƙarin yin garkuwa da shi.