NE

News Elementor

Jam’iyyar APC na son Peter Obi ya janye daga takarar 2027 kan bashin da ya ciyo lokacin yana Gwamnan Anambara

Kwamitin yakin neman zaɓen jam’iyyar APC ya nemi Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC a 2027, da ya janye daga takarar saboda zargin barin jihar da bashin dala miliyan 92.35.

Kakakin kwamitin, Dele Alake, ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Litinin, yana mayar da martani ga bayanan gwamnatin Anambra kan basussukan da aka ce gwamnatin Obi ta karɓa.

Gwamnatin jihar ta ce gwamnatin Obi ta karɓi bashin waje na dala miliyan 123.77 a cikin shekaru takwas da ya yi yana mulki, inda dala miliyan 92.35, kwatankwacin Naira biliyan 127.37, suka rage a matsayin basussuka har zuwa 30 ga Yuni 2026.

Ta ce an yi amfani da basussukan wajen ayyukan kiwon lafiya, ilimi, noma, kula da zaizayar ƙasa da sauran ayyukan ci gaba.

Sai dai Obi ya musanta hakan, yana cewa ya bar Anambra ba tare da bashin da ake binsa ba, tare da cewa bai bar bashin albashi, fansho, alawus ko kuɗin ’yan kwangila da aka kammala ayyukansu ba.Alake ya ce bayanan gwamnatin Anambra sun saba wa ikirarin Obi.

Ya kuma zarge shi da rashin biyan wasu ma’aikatan gwamnati albashi a lokacin mulkinsa.

APC ta ce Obi ya taɓa yin alkawarin janyewa daga takarar shugaban ƙasa idan aka tabbatar da cewa ya bar Anambra da basussuka, inda ta bukaci ya cika wannan alkawari.

Sai dai rikicin ya ci gaba da kasancewa tsakanin Obi da gwamnatin Anambra, yayin da tsohon gwamnan ya nemi gwamnatin jihar ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa ya bar mata bashin da ake zargi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM