NE

News Elementor

Atiku ya ce raba wa matasan APC motocin alfarma cin mutuncin talakawan Najeriya ne

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya soki rahotannin da ke cewa an raba motocin alfarma na SUV ga shugabannin matasan jam’iyyar APC.

Atiku, wanda yake neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da fadar shugaban ƙasa su bayyana inda kuɗin sayen motocin suka fito.

Rahotanni sun nuna cewa motocin na shekarar 2026 ne, kuma kowacce tana da darajar sama da naira miliyan 150. An ce uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ce ta bayar da motocin.

Atiku ya ce ’yan Najeriya suna da haƙƙin sanin ko an sayi motocin da kuɗin uwargidan shugaban ƙasa ne, gudummawar wasu mutane ko kuma kuɗin gwamnati.

Ya tambayi dalilin kashe makudan kuɗi wajen siyasa a lokacin da jama’a ke fama da rashin abinci, tsadar sufuri da sauran buƙatun yau da kullum.

Haka kuma, Atiku ya ce ya kamata gwamnati ta bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur, musamman ganin yadda talakawa ke ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM