Shugaban matatar man fetur ta Dangote, Aliko Dangote, ya ce daga gobe Talata, dukkanin gidajen man da ke siyen man fetur daga wurinsa za su fara siyar da litar mai kan naira 739.
Dangote ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, inda ya sanar da cewa, matatar ta rage farashin man fetur daga naira 828 zuwa naira 699.
Matatar ta rage farashin litar man da kusan naira 125.
Sabon farashin ya fara ne daga ranar 11 ga watan Decemba, wanda shi ne ragin farashi na 20 da matatar ta gudanar a wannan shekara.
Da ya ke zantawa a harabar matatar da ke birnin Legas, Dangote ya yi kira ga wakillan kungiyar IPMAN da su rinka siyen man fetur daga matatarsa, inda ya jaddada kudurinsa na ci-gaba da siyar da man feturin kan naira 699.
