Manyan kungiyoyin kabilu a Nigeria da suka kunshi Afenefere, Ohaneze da Matasan Arewa, sun goyi bayan kiraye-kirayen kafa yan sandan jihohi a kasar nan.
A wata zantawa da manema labarai, kungiyoyin sun bayyana kwarin-guiwa kan cewa, kafa yan sandan na jihohi zai taimaka wajan dakile matsalolin tsaro da ake fuskanta.
Da aka tuntube mai Magana da yawun kungiyar kabilar Yarbawa ta Afenefere, Comrade Jare Ajayi, ya ce Nigeria ta isa ta kafa yan sandan jihohi, sabanin yadda wasu alumma ke bayyana fargaba akai.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo, Mazi Okechukwu, ya ce kafa yan sandan jihohi ne kadai hanyar da za a bi wajan dakile zubar da jini, amma kuma ya ce wasu gwamnonin arewa za su iya amfani da yan sandan domin kayar da shugaba Tinubu a zaben 2027.
Shi kuwa, shugaban kungiyar Matasan Arewa, Alhaji Shettima Yerima, ya ce ta’addancin da ke faruwa a yankin arewa maso gabas, da satar mutane a arewa maso yamma, da kuma rikicin kabilanci a arewa ta tsakiya, na bukatar mataki na musamman da zai samar da yan sandan yanki matsawar ana son magance matsalolin.
