
Makarantun gwamnati a Jihar Kano na fuskantar matsanancin ƙarancin malamai da kuma ƙarancin ajujuwa, inda aka gano cewa malami ɗaya yana koyar da ɗalibai har 105 a makarantun firamare, bisa ga sakamakon ƙidayar makarantu ta shekarar 2024/2025.
Rahoton ƙidayar ya nuna cewa rabon ɗalibi zuwa malami a makarantun nazari da firamare na gwamnati ya kai 105:1, yayin da a makarantun sakandire na ƙaramar sakandare aka samu 50:1, sannan a manyan sakandire ya kai 37:1.
A cewar Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), adadin da ya dace na ɗalibi ga kowane malami a matakin firamare shi ne ɗalibai 25 ga malami ɗaya.
Sai dai kuma dokar ilimi ta Najeriya ta tanadi ma’auni na 1:25 ga matakin nazari, 1:35 ga firamare, da 1:40 ga sakandire.
Duk da haka, yawancin makarantun firamare na gwamnati, musamman a biranen da ke da yawan jama’a, suna aiki sama da waɗannan ƙa’idojin saboda cunkoso da ƙarancin malamai.
Ko da yake an fitar da rahoton ƙidayar makarantu na Kano a watan Disamba 2025, Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta tabbatar cewa shi ne sabon rahoto na ƙarshe da ake da shi kan fannin ilimi.
Wadannan alƙaluma na fitowa ne a daidai lokacin da ake da ɗalibai sama da miliyan 5.6 a makarantun gwamnati a faɗin jihar.