Jam’iyyar ADC ta soki shugaba Bola Tinubu kan furucinsa cewa a shirye yake ya “yi duk mai yiwuwa a fagen siyasa, tana mai cewa ya kamata ya mayar da hankali wajen murkushe ’yan ta’adda maimakon fafatawa da ’yan adawa.
A cikin wata sanarwa da sakataren Ylyaɗa Labaran jam’iyyar na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta bayyana cewa abin damuwa ne yadda shugaban ƙasar ya yi wannan furuci yayin ganawarsa da mambobin taron limaman cocin Katolika na Najeriya, alhali ƙasar na ci gaba da fuskantar tabarbarewar matsalar tsaro, ciki har da harin da aka kai ƙauyen Naridon da ke jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 30.
Jam’iyyar ta bayyana Tinubu a matsayin mai fitar da sanarwa kawai, tana mai cewa shugaban ya yi tsokaci kan matsalar tsaro, amma ya koma yaƙi da ’yan adawa.
Ta kuma zargi gwamnatinsa da mayar da martani ga hare-haren ta hanyar fitar da sanarwar Ala wadai kawai, maimakon ɗaukar matakan gaggawa da suka dace.