NE

News Elementor

Sardaunan Sokoto Alhaji-Alhaji ya rasu yana da shekaru 88 a duniya

Rahotanni daga majiyoyi masu alaƙa da iyalansa, sun tabbatar da cewa dattijon ya riga mu gidan gaskiya ne a safiyar yau Alhamis, a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja, bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.

Marigayin, shi ne ke riƙe da babban muƙamin sarautar Sardaunan Sokoto bayan rasuwar Sir Ahmadu Bello a shekarar 1966.

Alhaji Abubakar Alhaji ya yi aiki a matsayin Ministan Tsare-tsare da Kuɗi na ƙasa a lokacin mulkin soja ƙarƙashin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Haka zalika, ya taɓa zama babban jakadan Najeriya a ƙasar Birtaniya, daga 1992 zuwa tsakiyar 1996.

Shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ne ya naɗa shi wannan muƙami nan da nan bayan ya cire shi daga kujerar Ministan Kuɗi a shekarar 1992.

Gwamnatin mulkin soja ta Janar Sani Abacha ce ta maye gurbinsa a wannan lokacin. Bayan saukarsa daga wannan kujera ne kuma aka naɗa Ambasada Uche Okeke a matsayin wanda ya gaje shi a ofishin jakadancin da ke birnin Landan.

Marigayi Alhaji Abubakar Alhaji, jika ne na jinin masarauta kai-tsaye daga tsatson Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM