Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce dalilin da ya sa ya koma jam’iyyar Accord daga jam’iyyar Peopl PDP shi ne domin kare kansa da tabbatar da zaman lafiyar jihar.
Da yake jawabi a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Adeleke ya ce bai yi watsi da PDP ba, wacce har yanzu ya ce yana mutunta ta, sai dai ya fifita ci gaba da zaman lafiya da kuma bunƙasar jihar Osun.
“Ba gaskiya ba ne cewa na yi watsi da PDP. Ina son PDP, amma dole ne in kare kaina. Dole ne in tabbatar na kare jihata saboda kyakkyawan aikin da muke yi domin mu ci gaba,” in ji shi.