Matatar man fetur ta Dangote ta kara farashin mai, inda a yanzu kamfanin MRS zai rinka siyar da litar mai kan naira 839 a fadin kasar nan.
Karin na zuwa ne bayan kammala garabasar karshen shekara da matatar ta gudanar domin saukakawa yan Nigeria a lokacin shagulgula sakamakon matsin da magidanta ke fuskanta.
A tsawon lokacin na karshen shekara, matatar Dangote ta ce ta dauki manyan matakai domin saukaka harkokin man fetur, ciki har da rage farashi domin saukakawa alumma.
To sai dai, a karkashin sabun farashin na yanzu, matatar ta ayyana naira 799 daga naira 699 na baya, matakin da ta ce ya zama wajibi domin ta ci-gaba da gudanar da harkokinta yadda ya dace.
Duk da rage farashin na farko, matatar ta ce gidajen mai da dama sun ki sassauta nasu farashin, lamarin da ya sa alumma ba su amfana da wannan garabasar ba.