NE

News Elementor

Amnesty International ta Nuna damuwa Kan Take Ƴancin Faɗar Albarkacin Baki a Kano

Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana damuwa kan abin da ta kira karuwar kamawa, tsarewa da tsoratar da mutane a Kano saboda sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Amnesty International ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba.

Kungiyar ta zargi hukumar DSS da kamawa ko gayyatar wasu domin yi musu tambayoyi kan ra’ayoyinsu na sukar gwamnati, lamarin da ta ce yana haifar da fargaba da takura wa sararin dimokuraɗiyya a jihar.

Amnesty ta kawo misalan wasu da aka kama ko aka tsare, ciki har da Abba Ibrahim Hussain, wanda ta ce an kama shi a gidansa, da kuma wasu masu amfani da kafafen sada zumunta da aka tsare na ɗan lokaci saboda sukar gwamnan.

Haka kuma, akwai Aminu Warkal da aka rawaito cewa, jami’an tsaro sun gayyace shi inda ya shafe awanni 4, sai Samir Hanga shi ma da ake zargi da sukar Gwamnan da DSS suka gayyata.

Sauran waɗanda aka kama sun hada ra Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda da Saifullahi Abubakar.

Kungiyar ta jaddada cewa sukar shugabanni ko yin barkwanci a kansu ba laifi ba ne a tsarin dimokuraɗiyya, tare da kira ga hukumomin Najeriya da su mutunta tare da kare ‘yancin faɗar albarkacin baki na kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM