NE

News Elementor

An ƙwato dabbobi 1,000 da aka sace a wani sabon farmaki kan ƴan bindiga a jihar Kogi

Gwamnatin Jihar Kogi tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Najeriya, hukumomin tsaro da masu sintiri na al’umma sun samu nasarar ƙwato kimanin dabbobi 1,000 da aka sace a ci gaba da kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Fanwo ya ce farmakin ya mayar da hankali ne kan ragowar ƙungiyar marigayi shugaban ƴan bindiga, Kachalla Ibrahim Battijo, da kuma wasu ƙungiyoyin masu satar shanu da ke aiki a cikin Jihar Kogi da sauran yankin Arewa ta Tsakiya.

Ya ƙara da cewa an samu nasarar ƙwato dabbobin ne sakamakon sahihan bayanan sirri da aka samu cikin lokaci, waɗanda Rundunar Sojin Najeriya ta Brigade ta 12, dakaru daga Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA), Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Rundunar ‘Yan Sanda, masu sintiri na al’umma da mafarauta suka yi aiki a kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM