NE

News Elementor

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Babban Dilan Kwaya

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, sun kama wani tsohon dila kwaya mai shekaru 80, Jeremiah Isaiah Nkanta bayan da ya dawo gudanar da harkallar haramtattun kayan maye kusan shekara uku bayan ya gama zaman gidan yarin da aka yanke masa bisa aikata irin wannan laifi.

A cewar hukumar, Nkanta, kasurgumin dilan kwayar, tun da farko an kama shi ne a ranar 14 ga watan Disambar 2022, inda aka gurfanar da shi a gaban babar kotun tarayya da ke garin Uyo na jihar tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari.

Dattijon da ya ki sauya halinsa, hukumar ta ce Nkanta ya koma ruwa biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka samu, jami’an na NDLEA a ranar Assabar, 10 ga wannan wat ana Janairun wannan shekara, sun bi sawu tare da kama tsohon dilan kwayan a gidansa da ke kauyen Akwa-Ibom dauke da kilo giram 5.7 na kwayar Skun.

A wani aikin na daban kuwa duk a jihar Akwa-lbom, jami’an NDLEA, da ke rangadi a kan titin Oron zuwa Ibaka, sun cafke wani dan kasuwa mai suna Ani Onyebushi Romans wanda ke kan hanya zuwa Kamaru dauke da wata dilar tufafin sawa.

To saidai, bayan gudanar da bincike, an gno kwayar tramadol mai nauyin kilogram 5.3 sunke a cikin tufafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM