NE

News Elementor

An jiyo karar sabbin harbe-harbe da abubuwan fashewa a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar da sanyin safiyar Asabar

Rahotannin da gidan talabijin na Al-Jazeera ya tattara na cewa an jiyo karar harbe-harbe da abubuwan fashewa a wasu sassan Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar, da sanyin safiyar Asabar, kamar yadda shaidun gani da ido biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, yayin da har yanzu ba a san musabbabin lamarin ba.

Wata majiya daga bangaren jami’an tsaro ta shaida wa Reuters cewa wasu da ta bayyana a matsayin “’yan ta’adda” sun kai hari filin jirgin saman Diori Hamani na birnin, tare da yunkurin kutsawa cikin yankin tsaron da ke kewaye da fadar shugaban kasa.

Bana Wagana Ibrahim, mamba a Majalisar Shawara ta Nijar kuma dan majalisa a Majalisar Kungiyar Kasashen Sahel (AES), ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa maharan sun kai hari sansanin soja na Base 101, daya daga cikin manyan sansanonin soji a Niamey, amma jami’an tsaro sun sake kwato iko da wurin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM