NE

News Elementor

Ina matuƙar son matata har ta kai ba na iya mayar da hankali a wurin aikina— Miji

Wani uba mai ’ya’ya biyu ya bayyana cewa tsananin soyayyar da yake yi wa matarsa ta shafi yadda yake mai da hankali wajen gudanar da aikinsa.

Aminu Kabiru ya bayyana hakan ne a gaban wata Kotun Shari’a da ke Kaduna, a Jihar Kaduna, yayin da yake mayar da martani kan bukatar matarsa da suka rabu, wadda ta nemi a raba aurensu ta hanyar Khul’i.

A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), Aminu ya shaida wa kotun cewa ƙaunar da yake yi wa matarsa ta yi masa yawa matuƙa, har ta kai ga shagaltar da shi daga aikinsa tare da rage masa damar samun kuɗin shiga.

Wanda ake ƙara ya roƙi kotun da ta ba shi ƙarin lokaci domin ya sasanta da matarsa, yana mai cewa ya kamata a ceto aurensu saboda ƙananan ’ya’yansu.

Ya buƙaci kotun ta yi la’akari da jin daɗin yaran, waɗanda dukkansu ba su kai shekara biyu ba.

Sai dai matar tasa, ta hannun lauyanta, Abubakar Jibril, ta dage cewa ba ta son ci gaba da zaman auren.

Jibril ya shaida wa kotun cewa matar ta kwashe watanni takwas tana zaune a gidan iyayenta, ba tare da mijin nata ya ba ta kulawa ko tallafin da ya dace ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM