Dubun wani ɗan kasuwa da ke sayar wa al’umma gurɓataccen garin madara ta cika a Jihar Katsina.
’Yan sndan sun kama ɗan kasuwar mai suna Ibrahim Muhammad, mazaunin Ƙaramar Hukumar Funtua, ne bisa zargin yaudarar al’umma da sayar da guɓataccen garin madarar a matsayin mai inganci.
Sanarwar da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar ta ce masu sa ido na rundunar sun cafke wanda ake zargin ne a ranar 14 ga Yuni.
’Yan sandan sun bayyana cewa ɗan kasuwar yana sane da cewa garin madarar ta lalace, amma duk da haka ya sake zuba ta a cikin sababbin buhuna, ya ci gaba da sayar wa jama’a, lamarin da suka ce babban barazana ne ga lafiyar al’umma.
Ta bayyana cewa yin hakan ya saɓa wa tanade-tanaden Dokar Abinci da Magunguna, Cap F32, ta shekarar 2004, wadda aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2021.
Jami’an rundunar sun kuma kama buhuna 10 na guɓataccen garin madara da aka sake zubawa a sabbin mazubai.
Rundunar ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
A wani ɓangaren kuma, Kwamishinan ’Yansandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargin zai iya zama barazana ga tsaro ko lafiyar jama’a.