Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci yan jarida su yi amfani da damarsu domin karfafa dimukradiyya a kasar nan.
Da yake zantawa yayin kaddamar da littafin tarihin rayuwar wani sharararren dan jarida, Babajide Kolade-Otitoju a Abuja, Shettima ya ce ingantuwar tsarin dimukradiyya ya ta’allaka ne kan gudummawar kafafen yada labarai.
Mataimakin shugaban ya ce ba rashin abin fada ba ne ke haifar da komabaya a cikin alumma illa rashin samun jajirtattun mutane da za su rinka jagorantar jama’a wajan bayyana ra’ayinsu.
A wani bayani da mai Magana da yawunsa, Stanley Nkwocha ya fitar, Shettima ya kuma jaddada cewa, dimukradiyya ta fi karfin a kan zabuka da hukumomi.