Ana fargabar kimanin mutane 40 sun rasa rayukansu bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da manoma zuwa gonakinsu na shinkafa ya kife a garin Gorau, Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne a lokacin da waɗanda lamarin ya rutsa da su ke ƙoƙarin tsallaka wani rafin ruwa domin zuwa gonakinsu.
Rahotanni sun ce mafi yawan mutanen da ke cikin kwale-kwalen yara ne masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15.
Wani ganau ya bayyana cewa sama da mutane 70 ne ke cikin kwale-kwalen lokacin da ya kife, jim kaɗan bayan ya tashi.
An ce Dagacin garin yana cikin mutanen da ke cikin kwale-kwalen, amma an yi nasarar ceto shi.
Wani ɗan jarida na yankin, Sharhabilu Yahuza Kiliya, wanda yake wurin da lamarin ya faru, ya ce ya zuwa yanzu, an gano gawarwaki kusan 40, yayin da aka ceto mutane shida, ciki har da dagacin garin.
A cewarsa, waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da masu gonaki da ma’aikatan da aka ɗauka domin aikin girbin shinkafa.