NE

News Elementor

Kwankwaso ya yi kira a gudanar da bincike kan hatsarin kwale-kwale a Sokoto

Tsohon Gwamnan Kano kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC a 2027, Rabiu Kwankwaso, ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu a hatsarin kwale-kwale da ya afku a Gorau, karamar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.

Kwankwaso ya bayyana hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a matsayin abin takaici, tare da yin kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin.

A cewar rundunar ‘yansandan jihar, mutane 77 ne ke cikin kwale-kwalen da ya kife yayin da yake dauke da manoma da sauran fasinjoji zuwa gonakinsu.

Ya zuwa yanzu, an gano gawarwaki 46, yayin da aka ceto mutane 15 da ransu, sannan ake ci gaba da neman wasu 16 da suka bace.

Kwankwaso ya kuma yaba wa jami’an tsaro, masu aikin ceto da masu ruwa na yankin bisa kokarin da suke yi na ceto wadanda suka tsira da kuma gano wadanda suka bace.

Ya bukaci hukumomi su dauki matakan tsaro na musamman a hanyoyin ruwa domin hana sake aukuwar irin wannan mummunan hatsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM