NE

News Elementor

Ana jimamin mutuwar matasan Sokoto 9 da suka rasu yayin da suke kan hanyar zuwa Legas domin neman ingantacciyar rayuwa

Jihar Sakkwato ta shiga cikin alhini bayan rasuwar wasu matasa tara daga Ƙaramar Hukumar Yabo, waɗanda suka rasa rayukansu a wani mummunan haɗarin mota yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Legas domin naman kuɗi.

Lamarin ya jawo ta’aziyya daga sassa daban-daban na jihar da ma ƙasa baki ɗaya, inda mutane da dama suka bayyana cewa wannan iftila’i wata alama ce ta irin ƙalubalen da dubban matasan Najeriya ke fuskanta, wanda ke tilasta musu barin garuruwansu domin neman abin dogaro da kai.

Da yake mayar da martani kan wannan ibtila’i, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Yabo/Shagari, Hon. Umar Yusuf Danmaje Yabo, ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar matasan, yana mai cewa sun kasance matasa masu cike da burin rayuwa waɗanda mafarkansu suka ƙare cikin wannan mummunan haɗari.

A cikin saƙon ta’aziyyar da aka rabawa manema labarai a Sakkwato, ɗan majalisar ya ce haɗarin ya jefa iyalai, abokai da al’ummar Yabo baki ɗaya cikin jimami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM