NE

News Elementor

Atiku ya bukaci a gaggauta sakin masu zanga-zangar da aka kama kan sanya rigunan #TinubuMustGo

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci a gaggauta sakin ’yan Najeriya biyar da aka ce an kama a Jihar Borno bisa zargin sanya riguna masu dauke da kalmomin “Tinubu Must Go”.

Ya ce idan taken siyasa ne ya sa aka tsare su, to wadanda suka bayar da umarnin tsarewar dole ne su yi bayanin yadda sanya riga zai zama laifi a tsarin dimokuradiyya.

A cikin wata sanarwa da hadimin Atiku kan sha’anin yada labarai Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce Shugaba Bola Tinubu ya taba tsayawa tare da ’yan Najeriya da ke zanga-zangar adawa da tsadar man fetur a lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, amma a yanzu yana jagorantar wani yanayi na tsadar rayuwa da ya sanya man fetur, abinci, sufuri da wutar lantarki suka yi tsada matuka.

Atiku ya bukaci hukumomin da abin ya shafa su bayyana inda ake tsare da mutanen, su ba su damar tuntubar iyalansu da lauyoyinsu nan take, sannan su sake su idan taken siyasa ne dalilin kama su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM