Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da cewa an naɗa shi ne domin raunana jam’iyyun adawa ta hanyar haddasa rikice-rikice a cikinsu.
Ya ce yadda hukumar ta tafiyar da rikicin shugabanci a jam’iyyar ADC na nuna hakan.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Litinin, wadda kuma Ofishin Yaɗa Labaran Atiku ya sanya wa hannu.
Ya yi zargin cewa idan har abin da ake zargi da INEC ya tabbata, hakan na nuna nuna son kai daga hukumar, kuma zai iya haifar da sabon rikici a cikin jam’iyyar ADC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Sanarwar ta biyo bayan ikirarin Nafiu Gombe, wanda ke bayyana kansa a matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC na Ƙasa, cewa ya yi nasarar loda sunayen ‘yan takarar jam’iyyar zuwa shafin tsarin rajistar INEC.