Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cewa ta sauya sabbin dokokin haraji a sirrance, inda ta nace kan cewa babu wani gyara da ta yiwa dokokin wanda majalisar tarayya ba ta amince da shi ba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da dan takarar shugaban kasa na jamiyyar LP a zaben da ya gabata, Peter Obi, da kungiyoyin fararen hulla sun bukaci a dakatar da aiwatar da dokokin.
Da ya ke zantawa da manema labarai, hadimin shugaban kasa kan sha’anin yada labarai, Mr Temitope Ajayi, ya ce babu wata sukar yan adawa da za ta hana aiwatar da dokokin a watan Junairu.
Ya ce har yanzu babu wata hukuma da ta fito fili ta yi zargin cewa an sauya dokoki, inda ya bayyana masu yada zarge-zargen a matsayin yan adawa dake kokarin haifar da rudani kan manufofin gwamnati.
A cewarsa, an samar da dokokin ne ta hanyoyin da doka ta tsara kuma za su fara aiki a ranar 1 ga watan Junairu mai zuwa, kazalika tuni aka umarci hukumomin da lamarin ya shafa da su fara shirye-shirye.