NE

News Elementor

Ɗan ƙungiyar asiri ya harbi ɗan uwansa saboda ya bar ƙungiyar

Ƴansandan Jihar Delta sun kama wani da ake zargi mamba ne na kungiyar asiri ta Eiye Confraternity, mai suna Oghenebuba Mamatime, bisa zargin harbin wani tsohon mamban kungiyar bayan ya bar kungiyar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, Bright Edafe, ya bayyana cewa wanda ake zargin yana cikin jerin mutanen da ‘yansanda ke nema saboda zargin hannu a ayyukan kungiyoyin asiri.

Ya ce an kama shi ne a ranar 21 ga Yulin 2026 tare da hadin gwiwar matasan garin Jesse.

Edafe ya ce kama wanda ake zargin ya biyo bayan korafin da wanda aka harba ya kai wa ‘yansanda, inda ya zargi Mamatime da harbin shi bayan ya yanke shawarar ficewa daga kungiyar asirin a yankin Jesse na jihar.

Binciken farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 2 ga Yulin 2026 a titin Ujomi da ke Jesse, lokacin da sabani ya kaure tsakanin mutanen biyu saboda yunkurin tilasta wa wanda abin ya shafa komawa cikin kungiyar.

A cewar kakakin ‘yansandan, binciken ya nuna cewa wanda ake zargin bai ji dadin matakin da tsohon mamban ya dauka na ficewa daga kungiyar ba, lamarin da ya haifar da takaddama kafin a harbe shi.

Ya kara da cewa, bayan kama Mamatime, jami’an tsaro sun kwato bindigogi uku kirar gida da kuma bindiga kirar gida mai harsashi guda daga hannunsa.

Edafe ya ce har yanzu wanda ake zargin na tsare a hannun ‘yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Haka kuma ya yi kira ga musamman matasa da su guji shiga kungiyoyin asiri da duk wani aikin da ya shafi su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM