An shawarci ɗalibai a Jihar Sokoto da su koyi harsuna da dama baya ga Turanci domin inganta sadarwa da faɗaɗa iliminsu.
Wannan shawara ta fito ne yayin kammala gasar ƙarshe ta shirin English 101 da Iconic FM Nigeria ta shirya.
A yayin jawabin kammala shirin, Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya taya waɗanda suka yi nasara murna tare da nuna gamsuwa da yadda ɗaliban suka nuna ƙwazo a gasar. Ya ce abin da ya gani ya burge shi ƙwarai, yana mai yabawa da ƙoƙarin da ɗaliban suka nuna.
Farfesa Junaidu ya ƙara da cewa ya kamata ɗalibai ba kawai su fahimci Turanci ba, har ma su koyi yadda za su yi magana da shi cikin ƙwarin gwiwa tare da amfani da shi yadda ya kamata.
A ƙarshe kuma ya tunatar da cewa Najeriya na da albarkar harsuna sama da 200, don haka ya kamata su ƙara koyo daga cikinsu gwargwadon iko.