
Fitaccen dan siyasar nan na Kano, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya nemi afuwar Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf bisa kalaman cin zarafi da ake zargin dan siyasar ya furta kan gwamnan.
A wani bidiyo da mai magana da yawun Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa, an hangi Dan Bilki Kwamanda wanda ya nuna kamar yana tsare yana bayanin neman afuwa.
Kwamanda ya ce kalaman nasa da ya yi a wani shirin Rediyo basa nufin cin mutunci, amma ya nemi afuwa ga waɗanda ke ganin cin mutunci ne.