NE

News Elementor

Tinubu Ya Gana Da Shugaban Rundunar Sojin Africom

Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da kwamandan rundunar sojin Amurika a nahiyar Africa, AFRICOM, General Dagvin Anderson, tare da manyan jami’an tsaron Amurika da Nigeria a birnin Abuja.

Tawagar ta AFRICOM ta ziyarci shugaban ne a jiya Lahadi, a wani bangare na kawancen da kasashen biyu ke yi a bangaren tsaro.

Ganawar ta samu halartar manyan jami’an tsaron Nigeria, ciki har da mai bada shawara kan sha’anin tsaron kasa, Nuhu Ribadu, da ministan tsaro, General Christopher Musa, da babban hafsan tsaro, General Olufemi Oluyede, kazalika da babban hafsan sojin kasa, Laftanar-General Waidi Shaibu.

Kazalika, akwai babban directan hukumar leken asiri ta Nigeria, Mohammed Mohammed, da babban directan hukumar tsaron farin kaya ta DSS, Tosin Ajayi, da kuma babban hafsan soji mai kula da tattara bayanan sirri, Laftanar-General Emmanuel Uandiandeye.

Duk da cewa, kawo yanzu babu cikakken bayani kan dalilin ganawar, amma tana zuwa ne daidai lokacin da ake karfafa dangantakar tsaro tsakanin Nigeria da Amurika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM