Gidan talabijin na Channel ya ba da rahoton cewa, A ranar Laraba, ne fusatattunun jama’a a garin Dansadau, da ke Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, suka farmaki ɗan majalisar na jiha tare da yi masa duk bisa zargin rashin kyautata wa al’ummar yankin da kuma watsi da jama’arsa.
Rahotanni sun ce ɗan majalisar, Kabiru Mikailu, wanda ke wakiltar Maru ta Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, ya sha duka ne a hannun mazauna garin, lokacin da ya raka Gwamna Dauda Lawal a wata ziyara mai cike da tarihi zuwa yankin da ke fama da matsaloli.
Mazauna yankin sun zargi ɗan majalisar da yin watsi da yankin tun bayan zabensa, inda suka ce bai taɓa ziyartar al’umma ko shiga harkokin jama’a ba a manyan bukukuwa.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce ɗan majalisar bai halarci bukukuwan Sallah a garin ba, haka kuma bai je ya jajanta wa iyalan da hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a yankin ba.
An ce jami’an tsaro ne suka shiga tsakani domin daidaita lamurra da kuma hana tagayyara shi.
Gwamna Dauda Lawal ya je Dansadau ne domin ƙaddamar da aikin sake gina titin Dansadau–Gusau mai tsawon sama da kilomita 90.
A yayin ziyarar, gwamnan ya kuma ba da umarnin sake ginawa da gyara Babbar Asibitin garin, tare da samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana domin inganta rayuwar al’umma.
Gwamnan ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar dawo da tsaro, sake gina muhimman ababen more rayuwa, da kuma inganta jin daɗin al’ummomin da matsalar tsaro ta shafa a faɗin Jihar Zamfara.
Haka kuma, Gwamna Lawal ya karɓi sarautar gargajiya ta Garkuwan Dansadau, inda Sarkin Dansadau, Alhaji Garba Muhammad, Sarkin Kudu Dansadau, ya yi masa rawani.