NE

News Elementor

Nijar, Mali Da Burkina Faso Na Cikin Kasashe 7 Da Amurka Ta Hana wa Shiga Kasarta Bisa Dalilan Tsaro.

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Donald Trump, ta sanar da sanya sabbin takunkuman hana shiga ƙasar ga wasu ƙasashe 7, ciki har Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar bisa dalilai na tsaro.

A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar, ta ce ƙasashe 7 da wannan doka ta shafa sun haɗa da Burkina Faso da Mali da Nijar da Sudan ta Kudu da Syria da masu riƙe da takardun sheda daga hukumomin Falasɗinu, sai kuma Laos da Saliyo waɗana a baya aka sanya musu dokar ta wucin gadi.

Fadar da White House ta ce wannan sabuwar doka da za ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa, an samar da ita ne don taimakawa wajen bai wa Amurkawa kariya daga duk wata barazanar tsaro.

Dama a watan Yunin wannan shekarar ne Trump ya sanya hannu kan wata dokar haramta wa ƴan wasu ƙasashe 12 shiga Amurka, tare da takaita ta wasu 7 da ta shafi masu yawon bude ido da ɗalibai da kuma ƴan kasuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM