NE

News Elementor

Dangote Ya Kai Ƙarar Tsohon Shugaban NMDPR, Farouk Ahmed, Gaban EFCC

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya kai ƙarar tsohon shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur ta Najeriya, NMDPR, Farouk Ahmed, gaban EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito wata sanarwa daga kamfanin Dangoten, cewa shugaban kamfanin ya shigar da ƙarar Farouk a shalkwatar hukumar ta EFCC.

A baya Dangote ya shigar da ƙarar Forouk gaban hukumar ICPC mai yaƙi da almundahana a Najeriya, domin bincikarsa kan zargin kashe dala miliyan biyar wajen karatun sakandiren ƴaƴansa a ƙasar Switzerland.

Wani abu da ake ganin ya sa Shugaban ƙasar Bola Tinubu sauke shi daga muƙamain nasa.

Sai dai a kwanakin da suka gabata ne Dangote ya janye ƙorafin nasa daga hukumar ICPC, kodayake hukumar ta ce za ta ci gaba da binciken nata.

Sanarwar Dangoten ta ce ta janye ƙorafin daga ICPC ne domin samun damar shigar da sabon ƙorafi gaban hukumar EFCC.

A ƙorafin nasa Dangote ya buƙaci EFCC ta binciki Farouk bisa zargin tafka almundana da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba, tare da gurfanar da shi a gaban kotu idan aka same shi da laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM