Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce zai maka Shugaban Hukumar Harajin Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, a kotu kan mukamin da aka ba shi a Kwamitin Kamfen na Shugaban Ƙasa na APC na zaɓen 2027.
Melaye, wanda ke cikin shugabannin jam’iyyar ADC a Kogi, ya ce akwai yiwuwar samun rikicin muradun aiki, ganin cewa Adedeji ma’aikacin gwamnati ne kuma aka nada shi Mataimakin Daraktan tara kudaden kamfen Tinubu.
Ya kuma soki matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na jagorantar kwamitin kamfen dinsa da kansa, yana mai cewa hakan na nuna rashin amincewa da wasu shugabannin APC.
Melaye ya ce zai garzaya kotu domin a tantance ko nadin Adedeji ya dace da dokokin aikin gwamnati da ka’idojin da’a na ma’aikatan gwamnati.
A jerin kwamitin kamfen da APC ta fitar, Tinubu ne Shugaban Kwamitin, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Shugaban APC na ƙasa Nentawe Yilwatda suka kasance Mataimakan Shugaban Kwamitin. An nada tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, Darakta-Janar, yayin da Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama Sakatare.
Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, shi ne Daraktan Tara Kudaden Kamfen, yayin da Zacch Adedeji aka nada Mataimakinsa.