Gamayyar Matasan Daliban Ilmi ta Jihar Sakkwato ta amsa gayyatar Sheikh Musa Ayuba Lukuwa, na gudanar da zaman tattaunawa da mukabala kan wani batu na ilimi da ya shafi Annabi Muhammad (S.A.W.).
A cikin wata takarda mai kwanan wata 19 ga Agustan 2026, wadda kungiyar ta aikewa Daraktan Hukumar DSS na Jihar Sakkwato, ta ce ta karɓi gayyatar cikin girmamawa da kyakkyawar niyya.
Kungiyar ta ce tana fatan zaman zai kasance wata dama ta musayar ilimi, bayyana hujjoji da ƙara fahimtar juna tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa.
Ta jaddada cewa manufarta ba ita ce haifar da rikici, gaba, ƙiyayya ko rarrabuwar kawuna tsakanin al’ummar Jihar Sakkwato ba. Maimakon haka, ta ce tana son ganin an gudanar da zaman cikin nutsuwa, hikima, adalci da mutunta juna, tare da bin ƙa’idojin tattaunawar ilimi.
Gamayyar ta ce tana maraba da gudanar da mukabalar matuƙar za a gudanar da ita cikin tsari da mutunci, inda kowanne ɓangare zai samu damar gabatar da hujjojinsa cikin ’yanci, ba tare da cin mutunci, zagi, tsoratarwa ko wani abu da zai iya haifar da tashin hankali ba.
Haka kuma, kungiyar ta ce ya dace a gudanar da zaman a ƙarƙashin kulawa da sa ido na hukumomin da suka dace, domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da bin dokokin ƙasa.
Ta ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa tattaunawar ta kasance ta ilimi ce, ba ta rikici ba.
A ƙarshen takardar, kungiyar ta ce bisa wannan fahimta, tana ba da shawarar a gudanar da zaman a ɗaya daga cikin wuraren da za ta gabatar. *Sai dai jerin wuraren da kungiyar ta bayar bai bayyana a shafin takardar da aka aiko ba.*
Gamayyar Daliban Ilimi a Jihar Sakkwato, sun amince da yin mukabala tare da Sheikh Lukuwa
Gamayyar Matasan Daliban Ilmi ta Jihar Sakkwato ta amsa gayyatar Sheikh Musa Ayuba Lukuwa, na gudanar da zaman tattaunawa da mukabala kan wani batu na ilimi da ya shafi Annabi Muhammad (S.A.W.).
A cikin wata takarda mai kwanan wata 19 ga Agustan 2026, wadda kungiyar ta aikewa Daraktan Hukumar DSS na Jihar Sakkwato, ta ce ta karɓi gayyatar cikin girmamawa da kyakkyawar niyya.
Kungiyar ta ce tana fatan zaman zai kasance wata dama ta musayar ilimi, bayyana hujjoji da ƙara fahimtar juna tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa.
Ta jaddada cewa manufarta ba ita ce haifar da rikici, gaba, ƙiyayya ko rarrabuwar kawuna tsakanin al’ummar Jihar Sakkwato ba. Maimakon haka, ta ce tana son ganin an gudanar da zaman cikin nutsuwa, hikima, adalci da mutunta juna, tare da bin ƙa’idojin tattaunawar ilimi.
Gamayyar ta ce tana maraba da gudanar da mukabalar matuƙar za a gudanar da ita cikin tsari da mutunci, inda kowanne ɓangare zai samu damar gabatar da hujjojinsa cikin ’yanci, ba tare da cin mutunci, zagi, tsoratarwa ko wani abu da zai iya haifar da tashin hankali ba.
Haka kuma, kungiyar ta ce ya dace a gudanar da zaman a ƙarƙashin kulawa da sa ido na hukumomin da suka dace, domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da bin dokokin ƙasa.
Ta ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa tattaunawar ta kasance ta ilimi ce, ba ta rikici ba.
A ƙarshen takardar, kungiyar ta ce bisa wannan fahimta, tana ba da shawarar a gudanar da zaman a ɗaya daga cikin wuraren da za ta gabatar. Sai dai jerin wuraren da kungiyar ta bayar bai bayyana a shafin takardar da aka aiko ba.