NE

News Elementor

Fadar shugaban ƙasa ta caccaki Atiku kan yunƙurin tayar da batun kwace kadarorin Tinubu a Amurka

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan yunƙurinsa na sake tayar da batun shari’ar kwace wasu kadarorin Shugaba Bola Tinubu a Amurka ta hanyar amfani da wani kamfanin masu neman goyon bayan siyasa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce matakin Atiku ya saɓa wa martabar Najeriya tare da nuna rashin girmama ikon ƙasar, yana mai cewa batun an riga an warware shi tun fiye da shekara 30 da suka gabata, sannan kotunan Najeriya da sakamakon zaɓen 2023 sun riga sun kammala kansa.

Onanuga ya zargi Atiku da kashe dala miliyan 1.2 wajen ɗaukar wani kamfanin na Amurka domin ya miƙa tsofaffin takardun shari’ar ga gwamnatin Amurka, yana mai cewa hakan ba zai canja ra’ayin ‘yan Najeriya ba.

Ya kuma buƙaci Atiku ya bayyana matsayinsa kan wasu tsofaffin binciken da hukumomin Amurka suka taɓa gudanarwa a kansa, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fi mayar da hankali kan neman goyon baya daga ƙasashen waje maimakon gabatar da mafita ga matsalolin Najeriya.

Sai dai Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ba ya damuwa da abin da ya kira “wasannin siyasa” na Atiku, yana mai jaddada cewa shugaban ƙasar na ci gaba da mai da hankali kan aiwatar da manufofin gwamnatin sa da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM