NE

News Elementor

Falana ya yi barazanar maka gwamnatin tarayya a kotu kan raba wa alƙalai kyautar gidaje

Fitaccen lauya mai kare haƙƙin bil’adama, Femi Falana, ya yi barazanar garzayawa kotu domin ƙalubalantar gwamnatin tarayya kan rabon sabbin gidajen alfarma ga alƙalai a unguwar Katampe da ke Abuja.

Falana ya ce matakin ya saɓa wa doka kuma nuna wariya ne, domin an fifita alƙalai yayin da sauran ma’aikatan gwamnati ba su samu irin wannan gata ba. Ya bayyana cewa ba ya adawa da samar wa alƙalai gidaje masu kyau, amma ya ce ya kamata a kula da sauran ma’aikatan gwamnati, ciki har da malamai na jami’o’i da ma’aikatan gwamnati da suka yi dogon aiki.

Har ila yau, ya soki yadda wasu tsoffin gwamnoni da suka koma majalisar dattawa ke ci gaba da more alawus da gidaje, yayin da ma’aikatan gwamnati ke yin ritaya ba tare da irin waɗannan gata ba.

Falana ya jaddada cewa daidaito a gaban doka ya kamata ya shafi kowa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba zai shigar da ƙara domin ƙalubalantar wannan tsari.

A baya dai, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa an gina gidaje 40 domin alƙalai a Katampe, kuma za a ba su ne bisa tsarin mallakar gida bayan amincewar Shugaba Bola Tinubu. Sai dai aikin ya fuskanci suka daga wasu da ke ganin tamkar cin hanci ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM