Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa tun bayan da ya zama shugaban majalisar bai taɓa ganin kasafin kuɗin majalisar dokoki ta kasa ba.
Akpabio ya yi wannan bayani ne yayin zaman majalisar bayan sanatoci sun dakatar da wata buƙata da ke neman sake fasalin tsarin bayar da kwangiloli a majalisar da kafa kwamitin kula da harkokin kwangila.
Ya ce ya dace sanatoci su fara fahimtar yadda ake tsarawa da kashe kasafin kuɗin majalisar kafin a yi maganar sauya tsarin bayar da kwangiloli.
Ya ƙara da cewa shugaban majalisar ba ya da cikakken iko kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen majalisar.
A nasa ɓangaren, tsohon kakakin majalisar wakilai kuma Sanatan Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya tabbatar da cewa a lokacin da yake kakakin majalisar wakilai yana da damar ganin kasafin kuɗin majalisar.
Wasu sanatoci, ciki har da Sanata Binos Yaroe da Sanata Yahaya Abdullahi, sun buƙaci a samar da ƙarin gaskiya wajen tafiyar da kasafin kuɗin majalisar, suna masu cewa ‘yan majalisar ba sa samun damar tantance yadda ake kashe kuɗaɗen majalisar.
Daga ƙarshe, Akpabio ya buƙaci mai gabatar da ƙudurin, Sanata Sunday Karimi, ya janye shi, kuma ya amince da hakan.