Farashin danyen mai ya sauka zuwa kusan dala 90 kan kowace ganga a kasuwannin duniya, bayan da Amurka da Iran suka dakatar da hare-haren da suke kai wa juna domin bai wa tattaunawar diflomasiyya damar ci gaba.
A ranar Litinin, farashin Brent Crude, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’aunin farashin danyen mai a duniya, ya ragu da kashi 6.76 cikin ɗari zuwa dala 90.24 kan kowace ganga.
Haka kuma, farashin US West Texas Intermediate (WTI) ya fadi da kashi 6.04 cikin ɗari zuwa dala 83.92 kan kowace ganga.
Rahotanni sun ce faduwar farashin ta biyo bayan dakatar da hare-haren da Amurka da Iran suka yi a ƙarshen mako, bayan kusan makonni biyu ana musayar hare-hare.
Jakadan Amurka majalisar Ɗinkin duniya, Mike Waltz, ya bayyana cewa Shugaba Donald Trump ya dakatar da hare-haren domin ba wa tattaunawar diflomasiyya damar samun ci gaba.
Shi ma wani babban jami’in gwamnatin Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ƙasar za ta dakatar da hare-harenta matuƙar Amurka ta ci gaba da tsayawa kan wannan matsaya.
A ranar 23 ga Yuli, farashin danyen mai ya haura dala 100 kan kowace ganga bayan rahotannin hare-hare kan wasu jiragen ruwa a Tekun Red Sea.
Karuwar farashin danyen mai ta yi tasiri a Najeriya, inda farashin man fetur ya ƙaru.A ranar 23 ga Yuli, matatar mai ta Dangote ta ƙara farashin fetur daga Naira 1,075 zuwa Naira 1,215 kan kowace lita, tare da ci gaba da sayar da fetur a cikin kuɗin naira.
Haka kuma, tun ranar 16 ga Yuli, masu shigo da man fetur sun bayyana shirin ƙara farashin fetur a ma’ajiyun ajiya daga Naira 1,230 zuwa Naira 1,350 kan kowace lita.