NE

News Elementor

Shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi Sanata Rufai Hanga da Sanata Kabiru Gaya zuwa jamiyyar APC

Hanga, wanda sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya a karkashin jamiyyar NDC, ya fice daga jamiyyar bayan sun raba gari da babban aminisa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Shi kuwa Gaya, sanata mai wakiltar Kano ta kudu, ya fice daga NDC tare da raba gari da darikar Kwankwasiyya, kuma gabanin hakan, dan jamiyyar APC kafin daga bisani ya hade da Kwankwaso a jamiyyar NNPP.

Hanga da Gaya sun rasa damarsu ta samun tikicin jamiyyar NDC a zaben fitar da yan takara, inda Kwankwaso ya yi musu yankan baya.

Ana ganin komawar manyan yan siyasar biyu a APC zai karfafa jamiyyar, tare da raunana tafiyar Kwankwasiyya a gabanin zabe mai zuwa.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi manyan yan siyasar biyu bisa jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin, inda za a shirya musu taro na musamman.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM