Sojojin Operation MESA da suka haɗa da jami’an Brigade ta 3 ta Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ’Yan Sanda, sun ceto mutane uku daga cikin biyar da aka sace a baya a ƙauyen Lakwaya da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai sabon hari a garin Lakwaya, inda suka sace mazauna garin guda biyar.
Da yake zantawa da Daily Trust, Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Ƙasa, Brigade ta 3, ya ce an riga an ceto mutane uku zuwa yanzu.
A cewar majiyoyin cikin gida, lamarin ya faru ne a daren Lahadi a ƙauyen Zurin Mahauta, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali.
Hakimin ƙauyen Zurin Mahauta, Murtala Mai Unguwa, ya bayyana cewa maharan sun shigo yankin ne cikin duhun dare, inda suka kwashi waɗanda suka sace zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Ya ƙara da cewa an sanar da jami’an tsaro nan take, kuma sun ɗauki mataki cikin gaggawa, yana mai cewa har yanzu ana ci gaba da ƙoƙarin bibiyar masu garkuwa da mutanen domin ceto sauran waɗanda aka sace.