NE

News Elementor

Gwamna jihar Kano Abba Kabir ya roki ƴan Qadiriyya su zaɓi Tinubu a babban zaɓen 2027

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga mabiya darikar Qadiriyya da al’ummar jihar da sauran ‘yan Najeriya da su ci gaba da bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa goyon baya gabanin zaɓen 2027.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya bayyana cewa Abba Kabir Yusuf ya yi kiran ne ranar Asabar yayin halartar taron Kadiriyya Maukibi na bana da aka gudanar a Kano.

Taron ya samu halartar manyan malaman addinin Musulunci, ‘yan siyasa da sauran manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar.

A cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, taron ya kasance wata dama ta ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da kuma goyon bayan jagorancin Shugaba Tinubu.

A yayin taron, an kuma ƙaddamar da sabon dandamalin Maukibi da gwamnatin jihar Kano ta gina. Wakilin Shugaba Tinubu, Hon. Ibrahim Kabir Masari, ne ya ƙaddamar da dandamalin.

Taron ya kuma samu halartar tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari, da tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, waɗanda suka yi jawabai daban-daban.

Maukibin Kadiriyya ya haɗa manyan malaman addini da ‘yan siyasa daga sassan Najeriya, tare da dubban mabiya ɗariƙar Kadiriyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM