NE

News Elementor

Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa — Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ce matakan tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka sun ceci Najeirya daga durƙushewar tattalin arziki da kuma kare Najeriya daga “wargajewa.”

Shettima ya yi wannan bayanin ne ranar Asabar yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya ziyarci Shugaba Tinubu a Legas.

Da yake kare matakan da gwamnatin ta ɗauka kan tattalin arziki, Shettima ya ce kuɗin ajiyar ƙetaren Najeriya ya gaza dala biliyan $3.9 a lokacin da gwamnatin ta fara aiki, yana mai bayyana tattalin arziƙin a matsayin wanda ke daf da durƙushewa kamar yadda aka samu a Venezuela.

“A lokacin da muka karɓi ragamar mulki, kuɗin ajiyarmu na ƙetare na ƙasa da dala biliyan $3.9 ne wanda bai isa a shigo da mai da shi na wata ɗaya ba,” in ji Shettima.

Ya ce Tinubu na da “jaruntaka da cikakken imanin” ɗaukar matakai irin na cire tallafin mai da kuma daidaita kasuwar canjin kuɗi.

“Cire tallafin mai da daidaita kasuwannin canji wasu matakai ne da ke da tasiri mai yawa.

“Tattalin arzikin na daf da durƙushewa. Ya ceci tattalin arzikin,” in ji mataimakin shugaban ƙasar.

“Ina son ‘yan Najeriya su gane wannan muhimmiyar gaskiyar. Muna kan hanyarmu ta zuwa Caracas. Ya ceci tattalin arzikin; ya ceci ƙasar daga wargajewa.”

‘Lokacin matsi ba ya tabbata har abada’

Yayin da yake cewa ya san mastin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, mataimakin shugabna ƙasar ya ce gwamnatin na aiwatar da tsare-tsare da ayyuka domin sawƙaƙa nauyin da ke kan ‘yan ƙasar.

“Mun san da wahalar da ‘yan Najeirya ke sha , amma lokacin masti ba ya tabbata har abada; mutane masu juriya ne ke ɗorewa,” in ji shi.

“Gwamnati za ta ƙddamar da shirye-shirye da ayyuka domin rage raɗaɗin mutane.”

Shettima ya ce gwamnatin za ta ƙaddamar da wasu shirye-shirye ciki har da na jigilar dijital a arewa maso yammacin ƙasar da adaidaita sahu mai amfani da lantarki a arewa maso gabashin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM