Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya yabawa tallafin da shugaban kasa Bola Tinubu ke bawa jihar wajan dakile matsalolin tsaro da inganta kiwon lafiya.
Gwamnan ya ce shugaban kasa ya kawo dauki cikin gaggawa lokacin da jihar Bauchi ke fama da barazanar ta’addanci.
Mohammad, wanda shi ne dan takarar Sanatan Bauchi ta kudu a jamiyyar APM, ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin jihar, lokacin da ya karbi bakuncin ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da ministan kudi da tattalin arziki, Taiwo Oyedele.
Rahotanni sun ce ministocin sun ziyarci jihar Bauchi ne domin kaddamar da cibiyar binciken cutuka ta zamani a asibitin koyarwa ta jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.
Mohammad ya ce ya ji dadin yadda gwamnatin tarayya ke bawa jihar Bauchi gudummawa, musamman a bangarorin da jihar ke bukata.