Kwamitin wanzar da zaman lafiya na kasa, ya bayyana damuwa kan yadda ake samun rikice-rikicen siyasa, da kalaman tunzura jama’a da kuma yada labaran karya, inda ya ce zuwa yanzu, yan siyasa sun aikata laifuka 60 da suka sabawa yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a watan da ya gabata.
A wani bayani mai dauke da sa-hannun shugaban kwamitin, General Abdulsalami Abubakar, da jagoran kwamitin, Dr Matthew Hassan Kukah, kwamitin ya yi gargaidn cewa, laifukan na barazana ga lamurran siyasa, kuma suna raunata amincin jama’a, kazalika da haifar da rikici a bayan kasa.
Bayanan da kwamitin ya fitar daga ranar 19 ga watan Agusta zuwa 19 ga watan Satumba, sun nuna cewa, batun yada labaran karya ne ya mamaye kaso 40 na laifukan da aka aikata wadanda suka sabawa yarjejeniyar ta zaman lafiya.
Sai kuma batun da ya shafi kai hari ga abokan adawa da kadarorinsu wanda ya zo na biyu a jerin laifukan da kaso 21.7, yayin da batun cin zarafi da amfani da jami’an tsaro wajan yiwa yan siyasa barazana ya zo na uku da kaso 16.7
Da yake tunatar da yan siyasa kan cewa, yarjejeniyar da suka sanyawa hannu babban alakwari ne da suka dauka, kwamitin ya yi kira ga rundunar yansandan Nigeria da hukumomin tsaro, su gudanar da bincike na musamman kan wadannan laifukan.